Likitoci sun yi famar ceto rayukan mutane da dama da suka samu munanan raunuka a ranar Litinin, lokacin da hayakin wuta ya buge su ko kuma ya makale da su a cikin gidajensu a wani babban bene na birnin New York. Mutane 19 da suka hada da yara 9 ne suka mutu a gobarar.